Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Damokaradiya, Siyasa, Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Najeriya


Joshua Chibi Dariye-Plato, Jolly Nyame-Taraba.
Joshua Chibi Dariye-Plato, Jolly Nyame-Taraba.

Kimanin makonni biyu bayan yi wa tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da takwaransa na jihar Taraba Jolly Nyame ahuwa, hankali ya karkata kan tasirin hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, da kuma rawar da gwamnati ke takawa a yunkurin yaki da cin hanci da Rashawa a Najeriya.

Ranar Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye da takwaransa na jihar Taraba Jolly Nyame ahuwa, wadanda da farko kotu ta yanke ma su hukumcin daurin shekaru 14 kowannen su a shekara ta 2018, bayan da kotu ta same su da laifin badakalar kuli da jimilar su ta kai Naira biliyan 2.22 tsakaninsu.

Gwamnatin Buhari ta yi wa tsofaffin gwamnonin ne ahuwa tare da wadansu fursunoni 159 bisa dalilai dabam dabam da suka hada da dalilan jinkai da kuma rashin lafiya.

Tsofaffin gwamnonin sun yi mulki daga shekara ta 1999 zuwa 2007. Da farko, wata kotu da ke zama a Abuja ta yankewa Dariye hukumcin daurin shekaru 14 amma kotun daukaka kara ta rage wa’adin zama gidan yarin zuwa shekaru 12, yayinda kotun kolin kasar ta goyi bayan hukuncin bayanda tsohon gwamnan Dariye ya daukaka kara. Kotun kolin ta kuma goyi bayan hukumcin daurin shekaru 12 da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame.

kotu-ta-yankewa-dan-abdulrasheed-maina-hukuncin-daurin-shekara-14

Kwanaki biyu bayan yiwa tsofaffin gwamnonin ahuwa, wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan harkokin mulki da al’amuran yau da kullum a Najeriya da ake kira Kungiyar fafatukar kare hakin ‘yan kasa da tabbatar da shugabancin kwarai da ake kira “the Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP)” ta shigar da kara tana kalubalantar yiwa tsofaffin gwamnonin ahuwa.

SERAP
SERAP

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta sake shawara ba tare da bata lokaci ba, ta janye afuwar da ta yi wa tsofaffin gwamnonin, yayinda kungiyar ta yi barazanar maka gwamnatin a kotu idan ba ta janye ba.

Tun sanar da yi wa tsofaffin gwamnonin ahuwa dai, ake ta tafka mahawara a ciki da wajen Najeriya. Lamarin da ake alakantawa da siyasa.

A hirar ta da Muryar Amurka, Naja’atu Mohammed wata mai kula da lamura a Najerya ta bayyana cewa, gwamnatin ta dauki wannan matakin ne da wata manufa da ba ta fita ta bayyanawa ‘yan Najeriya ba. Bisa ga cewarta, idan gwamnatin Buhari ta yafewa tsofaffin gwamnonin, ai ‘yan Najeriya da suka cuta ba su yafe ba sabili da haka bai kamata a sake su ba.

Shi ma a nashi tsokacin, shugaban kungiyar da ke sa ido kan harkokin mulki da neman ganin an yi adalci, Auwal Musa Rafsanjanni ya bayyana cewa, yi wa tsofaffin gwamnonin ahuwa maida hannun agogo baya ne a yaki da cin hanci da rashawa. Ya bayyana cewa, doka da shari’a suna cin talakawa ne kawai ganin yadda manyan ‘yan siyasa da masu hannu da shuni suke cin karen suba babbaka yayinda ake kuntatawa talakawa. Ya yi bayani da talakan da ya saci kwalayen indomi da kudinshi bai wuce Naira dubu 25 ba, domin ya rasa hanyar ciyar da iyalinshi, amma duk da bayanin da kuma sha’awar da masu hali baiwa su ka nuna ta tallafa wa mutumin da ke fama da talauci, aka yanke ma shi hukumcin dauri a gidan yari.

Farfesa Wole Soyinka wanda ya sami lambar yabo ta Nobel
Farfesa Wole Soyinka wanda ya sami lambar yabo ta Nobel

Fitattun ‘yan Najeriya da suka kushe wa yi wa tsofaffin gwamnonin ahuwa sun hada da fitaccen lauya kuma dan fafatukar kare hakkin bil’adama Femi Falana da fitaccen marubuci da ya sami lambar yabo ta Nobel Wole Soyinka wadanda suka yi Allah wadai da matakin da su ka ce ya saba hankali.

A hirar shi da manema labarai jim kadan bayan sanar da afuwar, Farfesa Soyinka ya bayyana cewa, wannan na nufin yaki da cin hanci da rashawar da gwamnatin Buhari ta ce tana yi “ya kare.”

A nashi tsokacin, fittacen lauya mai kare hakkin bil'adama Femi Falana ya bayyana cewa, ana murde tsarin shari’a domin kyautatawa ‘yan siyasa da muzantawa talakawa. Ya bayyana Afuwar da fasa kwai a fuskar Najeriya da ya ce zai dauki lokaci kafin ‘yan Najeriya su manta.

Fitaccen Lauya a nahiyar Afurka, Femi Falana, SAN.
Fitaccen Lauya a nahiyar Afurka, Femi Falana, SAN.

A sanarwar da ya fitar Falana ya ce, “Wannan ya fito daga shugaban da ya yi yakin neman zabe da hujjar yaki da cin hanci da rashawa, shugaban da ya sa dukan kwan shi a kwando daya, kwan ke nan guda daya da aka fasa a fuskokin ‘yan Najeriya da ba za su manta ba- ko su iya sharewa cikin sauri”

Falana ya kushewa banbancin da ake nunawa a fannin shari’a. Bisa ga cewar sa, ana kyale ‘yan siyasa da su ke cin hanci da rashawa su rika cin karensu ba babbaka.

Sai dai duk da kushe afuwar da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi wa tsofaffin gwamnonin, wadansu shugabannin al’umma sun yaba. Daga cikin wadanda suka goyi bayan afuwar akwai gwamnan jihar Beniwu Samuel Ortem, wanda kwanaki biyu kafin sanar da afuwar ya yi kira ga gwamnatin Buhari ta saki gwamnonin bisa hujjar cewa, sun koyi darasi. Bayan sanar da ahuwar, gwamnan da ya yi wannan kiran a wata hira da tashar talabijin ta Arise a Najeriya, ya yabawa gwamnatin shugaba Buhari da ya ke yawan suka kan harkokin tsaro, tare da jinjinawa dangi da abokan tsofaffin gwamnonin da su tsaya ma su.

Shi ma a nashi, lokacin, Rev Joseph Hayep mataimakin shugaban kungiyar Kiristoci reshen jihar Kaduna, ya ce yaki da cin hanci da rashawa zai yi tasiri ne kawai idan ana adalci ba tare da maida wadansu ‘yan lele, wadansu kuma ‘yan agola ba. Ya bayyana takaicin matsayin da wadansu ke ikirari da cewa, duk wanda ya shiga wata jam’iya ya hau tudun mun tsira.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

A wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Buhari a fannin harkokin sadarwa Garba Shehu ya fitar ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin kasa sashe na 175 lamba ta daya ya ba shugaban kasa ikon yin ahuwa. Bisa ga cewarshi, babu wata manufa ta siyasa dangane da yi wa gwamnonin ahuwa. Yace kasancewar su tsofaffin gwamnoni ba zai hana a yi masu ahuwa ba idan sun cancanta.

Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa, kwamiti na musamman da shugaba Buhari ya kafa domin tantance wadanda suka cancanta a nuna masu jinkai a yi masu ahuwa, ya yi wa fursunoni 412 tambayoyi daga ciki aka mika sunayen 162 ga majalisar zartaswa ta kasa, inda majalisar ta amince da yi wa 159 daga cikin su ahuwa.

efcc-ta-gurfanar-da-tsohon-babban-hafsan-sojin-najeriya-da-wasu-janar-2-a-kotu-bisa-zargin-badakalar-naira-biliyan-13

badakalar-kudi-efcc-ta-tsare-tsohon-shugaba-majalisar-dattawa

Daga cikin wadanda aka yi wa ahuwar tare da tsofaffin gwamnonin akwai Enitan Ransome-Kuti, tsohon kwamandan rundunar hadin guiwa da wata kotun soja ta musamman ta samu da laifin sakaci a yaki da Boko Haram a watan Janairu shekara ta 2015.

I zuwa yanzu, gwamnati ba ta fitar da cikakken jerin sunayen dukan mutanen 159 da aka yi wa ahuwa ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa fursunoni ahuwa ba. Ko a shekara ta 2020, Buhari ya yi wa fursunoni 41 a gidajen yari dabam dabam na kasar ahuwa daga cikin fursunoni 176 da kwamitin na musamman ya tantance. Wadanda gwamnatin Buhari ta yi wa ahuwar a wannan shekarar sun hada da Chief Anthony Enahoro, da Lt.-Col. Moses Effiong (rtd), Major E.J. Olanrewaju da kuma Ajayi Olusola Babalola wadanda duka suka rigamu gidan gaskiya, wadanda ahuwar ta janyo zazzafar suka, musamman ta Chief Enahoro da Prof. Ambrose Mofolorunsho Alli gwamnan tsohuwar jihar Bendel da aka yi wa ahuwa shekaru 37 bayan hambare gwamnatinsa a juyin mulki da kuma tuhumar shi da laifin cin hanci da rashawa.

A shekararar ta 2020 gwamnati ta kuma saki fursunoni 2600 da ke gidajen gyara hali a fadin kasar, sabili da barkewar annobar korona.

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Banda gwamnatin shugaba Buhari, a watan Maris, shekara ta 2013, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi wa tsohon gwamnan jihar Bayelsa marigayi Dipreye Alamieyesegha, ubangidansa na siyasa wanda Goodluck Jonathan ya yiwa mataimakin gwamna tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2005, kafin ya gaje shi a matsayin gwamnan bayan da aka cire shi daga mukamin sakamakon amsa laifin cin hanci da rashawa da aka tuhume shi da aikatawa.

‘Yan Najeriya da suka hada da fitattun ‘yan siyasa da shugabannin al’umma da su ka hada da tsohon shugaban Najeariya Olusugen Obasanjo sun kushewa Shugaba Goodluck Jonathan domin yin ahuwar da aka bayyana a matsayin kyautatawa ubandakinsa da raunana yunkurin yaki da cin hanci da rashawa.

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha (R),
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha (R),

Sai dai masu kula da lamura sun bayyana abinda ya banbanta ahuwar da shugaba Buhari ya yi wa tsofaffin gwamnonin wadanda gwamnati ta ce ta yi wa ahuwa bisa dalilan rashin lafiya da kuma shekarunsu na haihuwa, -wadanda dukansu sun haura shekaru 60-, da cewa, tsohon gwamnan jihar Bayesan ya yi nadama ya kuma amsa lafinsa nan da nan bai bari an bata lokaci da kudin gwamnati ana doguwar sharia’a ba, yayinda gwamna Dariya da takwaransa Nyame suka yi ta kalubalantar karar da EFCC ta shigar, da ta hada da karar EFCC da gwamna Dariya ya yi yana neman hukumar ta mayar mashi da kaddarorin da ta kwace da hukumar ta ce ya samu ta hanyar da ba ta kamata ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG