Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Badakalar Kudi: EFCC Ta Tsare Tsohon Shugaba Majalisar Dattawa


EFCC
EFCC

Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta fara yiwa tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim tambayoyi a kan zargin almundahana da karkatar da dukiyar jama’a.

Sanata Anyim wanda ya isa shelkwatar hukumar EFCC da ke unguwar Jabi a birnin Abuja da misalin karfe 3 na yammacin ranar Lahadi, ya shafe sama da sa'o'i 6 yana amsa tambayoyin jami’an hukumar inda rahotanni ke cewa ba’a bar shi ya koma gida ba a ranar Lahadin.

Ko da yake ba bu cikakken bayani a game da zarge-zargen da ake yi wa tsohon shugaban majalisar dattawan har lokacin hada wannan labarin, wata majiya da ke da masaniya a kan lamarin ta alakanta zuwan Anyim ofis din EFCC da zargin almundahanar da ta shafi tsohuwar ministar sufurin jiragen sama kuma sanata mai ci, Stella Oduah.

Majiyar ta kara da cewa an gano wani bangare na kudaden gyaran da ya kamata a yi a bangaren sufuri a lokacin da ya kai Naira miliyan 780, da ake zargin an karkatar da su zuwa wani kamfani da Sanata Anyim ke matsayin darakta a ciki kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Tsare shi din kuma na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka ambaci sunan sanata Stella Oduah a cikin badakalar takardun Pandora a matsayin daya daga cikin 'yan Najeriya 10 da ke boye dukiyarsu a wuraren da ake biyan haraji.

A makon jiya ne hukumar EFCC ta bayyana cewa ta fara binciken wasu mutanen da aka ambaci sunayen su a badakalar takardun na Pandora, ciki har da tsohon gwamnan jihar Anambra, Pete Obi, da sanata Stella Oduah da wasu da aka ambata a cikin rahoton.

XS
SM
MD
LG