Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Republican Trump Na Kokarin Tsamo Kansa daga Rikicin da Ya Tsunduma Ciki


Donald Trump na Jam'iyyar Republican

Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Republicans a nan Amurka, Donald Trump, na nan yana ta kokarin tsamo kansa daga rikicin da ya fada bayan da ya soki lamirin iyayen wani sojan Amurka da aka kashe a yakin Iraq, inda yanzu hatta kungiyoyin tsofaffin soja sun fito fili suna bayyana jin haushinsu da kalaman dan takaran.

Wani babban kusar majalisar dattawan Amurka wanda shi kansa tsohon soja ne da aka taba kamawa aka tsare a lokacin yakin Vietnam, Senator John McCain yace sam, bai yarda da kalaman da Donald Trump yayi ban a cewa a hana Musulmi kamar Kyaftin Humayon Khan shigowa Amurka ba.

Khizr Khan, iyayen Capt. Humayun S. M. Khan wanda ya rasa ransa a Iraqi da Trump ya wofantar, lamarin bai yiwa amurkawa dadi ba.
Khizr Khan, iyayen Capt. Humayun S. M. Khan wanda ya rasa ransa a Iraqi da Trump ya wofantar, lamarin bai yiwa amurkawa dadi ba.

Shima kansa McCain din bai tsira daga bakin Trump ba, wanda a can baya ya taba sukar lamirin McCain wai don an taba kama shi a lokacin yaki, inda yake cewa shi “ya fi son sojan da ba’a taba kama su a yaki ba.”

Duk wannan cece-kuccen na yanzu ya biyo ne bayan da iyayen shi Captain Khan, watau mahaifinsa Khizr da mahaifiyarsa Ghazala, suka bayyana a wajen babban taron tsaida ‘yar takara ta jam’iyyar Democrats, inda kuma shi Mr. Khan ya bayyana jin takaici da renin da Trump ke wa Musulmi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG