Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dandalin Fulani na Bayyana Matsalolin da Suke Fuskanta


Dinka cattle herdsmen in Abyei.
Dinka cattle herdsmen in Abyei.

Rigingimu da Fulani a sassan Najeriya sai yaduwa su keyi inda suna kashe mutane su ma ana kashesu. Kama daga Benue, Filato Edo , Oyo, Kogi har ma Katsina ko Kaduna, Taraba maganar daya ce, kashe-kashe da kone kone.

Fulani daga jihohi daban daban kama daga kudancin kasar zuwa arewa sun taru a Abuja a ofishin kungiyarsu ta Miyetti Allah inda suka tattauna kan matsaloli da yawan rigingimun da suka samu kansu ciki.

Wakilin Muryar Amurka ya ziyarci dandalin taron kuma ya samu ya zanta da su kan abubuwa da dama.

Zakari Yau Ibrahim da ya fito daga kudancin Najeriya yace abun da ya kawo su Abuja zargi wasu suka yi masu har ma aka kama 'ya'yansu a ka kulle. 'Yanbangan da suka kamashi sun zargeshi da sata, sun hakikance barawo ne. Bayan sun zagaya su kubutar da yaron hakan bai yiwu ba sai da suka kai kuka Abuja wurin sarkin Fulani wanda ya shi ma ya kai kuka wurin sifeton 'yansanda kafin a kawo karshen maganar. Zakari ya nuna cewa a na nuna masu kiyayya a kudancin kasar inda ake yi masu barna.

Baba Shehu yace a jihohin Oyo, Kogi, Ondo, Edo da wasu wurare ana yi masu wulakanci ana kama su kamar su ba 'yan Najeriya ba ne. Shi ma yace sun zo su godewa Oroji sarkinsu da sifeton 'yansanda. Yace abun da ya fi damunsu a Najeriya shi ne cin mutuncin da ake yi masu. Ko ruwa suka sha sai sun biya. Kasar da suke suna biya.

Dangane da karatun zamani, Zakaru Yau yace shi ya samu ya yi karatun firamare. An nuna masa cewa kila rashin yin karatun zamani ya cucesu. Karatun boko zai taimakesu idan zasu yi . Zakari yace yanayin da suke ciki ya sa basa karatu. Dole su yi kiwo suna tashi daga wannan wurin zuwa wancan wurin.

Ga cikkaken rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:55 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG