Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daniel Amokachi Na Jimamin Mutuwar Maradona


Daniel Amokachi (Hoto: Instagram)
Daniel Amokachi (Hoto: Instagram)

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya Daniel Amokachi ya bi sahun takwarorinsa a fagen wasan kwallo wajen nuna alhinin mutuwar shahararren dan wasa Diego Armando Maradona.

Amokachi wanda ya bugawa Super Eagles ta Najeriya wasa a tsakanin shekarun 1990, ya bayyana rasuwar Maradona a matsayin “ranar bakin ciki.”

“Ranar bakin ciki…… a yau na rasa aboki, shahararren dan wasa na kowane zamani Diego Armando Maradona, Allah ya sa ka huta, kana wuri mai inganci.” Amokachi ya rubuta da manyan harrufa a shafinsa na Instagram.

Sakon nasa na ne da hade da wani hoto da ke nuna Amokachin, Maradona da Mutiu Adepoju a lokacin da Najeriya take karawa da Argentina a gasar cin kofin duniya da aka yi a Amurka a 1994.

Argentina ta doke Najeriya da ci 2-1 a gasar wacce Brazil ta dauki kofin.

A ranar Laraba Maradona ya rasu sanadiyyar matsalar bugun zuciya.

Ya rasu yana dan shekara 60.

A ranar 30 ga watan Oktoba ya yi bikin cika shekararsa ta 60 inda a nan ma Amokachi ya taya shi murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Maradona ya kasance daya daga cikin mashahuran ‘yan wasa da duniya ba za ta taba mantawa da su ba, inda ya jagoranci kasar ta Argentina ta lashe kofin gasar duniya ta a 1986.

Daga baya, ya sha fama da matsalar yin mu’amulla da hodar iblis da matsananciyar kiba.

Wani lamari da ya kara sa Maradona ya yi fice shi ne kwallon da ya zira da hannu a ragar Ingila a zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin duniyar ta 1986, wacce ta haifar da takaddama a fagen kwallo na duniya.

Maradona ya kwashe sama da shekara 20 yana haskawa tare da nishandantar da ma’abota kwallo a duniya da wani irin salon lailaya kwallo da shi kadai ya kirkira kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Sai dai kimarsa a idon duniya ta fuskanci tagomashi saboda matsalar shaye-shaye da ya kasa daina wa da kuma rashin tabuka abin a- zo-a-gani a lokacin da aka ba shi jagorancin kungiyar kwallon kafar kasarsa.

Amma duk da haka, ya ci gaba da zama abin yabo a kasar ta Argentina da ke mutuwar son kwallo inda sukan yi mai kirarin “Pibe de Oro,” da harshen spaniya – kirarin da ke nufin “Yaro Dan Gwal,” ko kuma “Golden Boy,” a harshen Ingilishi.

Diego Maradona 1960-2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG