Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dattawan Arewacin Najeriya Sun Jaddada Adawarsu Da Mulkin Karba-karba


Kungiyar Dattawan Arewa

"Tun da akwai yawan jama’a da ake bukata a zabe, babu wani dalili da zai sa Arewa ta tsaya a mataki na biyu alhalin za ta iya neman matakin farko kuma ta sami nasara."

A baya-bayan nan dai an yi ta yawaita kiraye-kiraye kan batun yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba idan shugaban Najeriya da ke kan karagar mulki Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa na shekaru 8 a shekarar 2023.

Haka kuma jiga-jigan siyasa da suka hada da gwamnonin kudancin kasar sun yi ta yin kira kan a maida ragamar shugabancin Najeriya zuwa kudu inda wasu daga yankin ke fadi-tashin cewa ya zama wajibi mulki ya koma yankinsu, sabanin yadda wasu yan arewa ma ke hangen ci gaba da mulki bayan kamalla wa’adin shugaba Buhari.

To sai dai Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa babu laifi a cikin batun Arewacin Najeriya ta ci gaba da mulkin kasar a shekarar 2023 saboda tsarin mulkin dimokuradiyya ya bada dama.

A lokacin da yake jawabi a taron lakca kan shugabanci na tunawa Yusuf Maitama Sule, wanda reshen daliban gamayyar kungiyoyin Arewa wato CNG ya shirya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kakakin kungiyar dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa ba lalle ne sai wani yanki ne kadai zai samar da shugabanci ba bisa tsarin dimokaradiyya.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed
Dr. Hakeem Baba-Ahmed

Hangen na mutanen arewacin Najeriya dai ba ya rasa nasaba da la’akari da tsarin mulkin dimokuradiyya da ke amfani da yawan mutane wajen zabe da kuma baiwa duk wanda ke da yawan allumma damar mulkar kasashe.

Haka kuma, a yayin jawabinsa, Baba-Ahmed ya ce ba kuma dole ne sai an bi tsarin ba wa arewa mataimakin shugaban kasa ba a shekarar 2023, ya na mai cewa Arewacin kasar na da yawan jama’ar da za su iya tsayar da dan takarar shugaban kasa da suke bukata, kuma su sami nasara a zaben.

A cewarsa, ba za’a yi ta cinikayyar siyasa da arewa ba inda ya ce duk masu dabi’ar jiran lokacin zabe ya zo mutane su hau layi a raba musu kudi za su sha mamaki, don za’a fuskanci gaggarumin sauyi ba yadda aka saba gani ba a da a lokutan zabe.

Tsarin mulkin dimokradiyya a siyasance dai ya ta’allaka ne ga yawan kuma arewa na da yawan jama’a in ji shi.

Dakta Baba-Ahmed ya ce tun da akwai yawan jama’a da ake bukata a zabe, ba bu wani dalili da zai sa arewacin kasar ta tsaya a mataki na biyu alhalin za ta iya neman matakin farko kuma ta sami nasara.

Kazalika, Baba-Ahmed ya ce ba bu wanda zai iya yi wa Arewa barazana, ya na mai cewa kuskure ne masu tunanin za su iya sayen jama’a a lokacin zabe saboda yanayin matsin tattalin arzikin da kalubalen tsaro.

A wani taro da suka yi a watan Yulin da ya gabata, gwamnonin jihohin kudancin Najeriya tashi da matsayar cewa lallai ya kamata wanda zai gaji shugaba Muhammadu Buhari ya zama daga yankin kudancin kasar yake.

Gwamnonin sun kafa hujjar cewa tunda tsarin mulkin karba-karba tsakanin arewa da kudancin kasar shi ya samar da shugabannin baya-bayan nan da shugaba Buhari mai ci, kamata ya yi a ce mulkin ya koma kudu.

Akwai wasu manya a arewacin Najeriya da su ma suke goyon bayan wannan tsari na kara-karba duk da cewa kungiyar ta dattawan arewacin Najeriyar na adawa shi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG