Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dattawan Siyasa A Najeriya Sun Bukaci Buhari Ya Sanya A Hunnu Kan Sabuwar Dokar Zabe


INEC
INEC

Dattawan siyasa na kara karfafa kira kan sanya hannu ga sabuwar dokar zabe da ke kunshe da zaben 'yar tinke wajen tsayar da 'yan takara, da tura sakamako ta na'ura.

Yanzu haka dokar ta na gaban shugaba Buhari don sanya mata hannu ta zama doka, bayan amincewa da ita da majalisar dokokin tarayya ta yi, don amfani da ita a babban zaben 2023.

Tuni a ka fara fargabar gwamnoni kan iya yin kafar angulu ga dokar, ganin yadda hakan zai iya rage tasirin su a wajen tsaida 'yan takara.

Ga dattijon siyasar APC Musa Abubakar Danmalikin Kebbi, "amincewa da dokar ne mafita ga dimokradiyya Najeriya."

A cewar shugaban matasan PDP mai adawa, "duk wata dokar zabe ba za ta yi nasarar da a ke bukata ba sai hukumar zabe ta yi adalci."

Abun da ya fi damun dattijon siyasar NEPU Husseini Gariko shi ne yanda rashin tsayar da 'yan takara ta hanyar adalci ke ba wa 'yan jari hujja damar hayewa kan mukamai.

Ko da yake gabanin zaben shekarar 2019 shugaba Buhari bai sanya hannu kan gyaran dokar zabe ba da ya hada da sauya jerin zabuka inda masu mara baya ga kaucewar dokar ke cewa ta na da kulle-kullen hana shugaban tazarce ne.

A wani bangaren kuma tuni Hukumar zabe ta kasa ta bayyana cewar za'a gudanar da zaben shekarar 2023 na shugaban kasa da kuma ‘yan majalisar wakilai da dattijai da a ranar 18 ga watan Fabrairu.

Sanarwar ta ci gaba da cewar zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na jahohi kuma zai kasance ranar 4 ga watan Maris na shekarar ta 2023.

Wadanda suka sami nasara kuma za a rantsar da su a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

XS
SM
MD
LG