Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Diego Maradona Ya Nuna Alamun Murmure Daga Tiyatar Da Aka Yi Masa


Maradona Argentina Casa Rosada

Tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Diego Maradona na murmurewa cikin sauri bayan tiyatar da aka yi masa a kwakwalwa.

Shahararren dan wasan kwallon duniya Maradon ya na nuna alamun murmurewa wuni daya bayan tiyatar kwakwalwa da aka yi masa a Argentina kasarsa ta asali.

Maradona dan shekaru 60, wanda ya jagoranci kasarsa ta lashe gasar cin kofin duniya a Mexico a shekarar 1986, ya bukaci tiyatar ne saboda matsalar zubar da jinni na kwakwalwa da ya fuskanta.

Likitansa Dr. Leopoldo Luque ya ce Diego na samun sauki yadda ya kamata.

An dai kwantar da Maradona ne a karamin asibitin Ipensa a babban birnin Argentina Buenos Aires a ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba sakamakon karancin jinni da ruwa a jikinsa.

Tsohon dan wasan na tsakiya na Barcelona da Napoli, zai ci gaba da zama a asibitin da ke babban birnin kasar akalla sa’o’i 48 yayin da ya ke ci gaba da murmurewa.

Facebook Forum

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG