Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Direban Shugaba Buhari Ya Rasu


Sa'idu Afaka
Sa'idu Afaka

Sa'idu Afaka ya rasu ne a asibitin fadar shugaban kasar da ke Abuja, bayan fama da ya yi da rashin lafiya na wani tsawon lokaci.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’aziyya ga iyalan Afaka bisa rasuwar direbansa, Sa’idu Afaka wanda ya mutu a asibitin fadar a ranar Talata bayan doguwar rashin lafiya.

Shugaba Buhari, wanda kuma ya jajantawa gwamnati da jama'ar Jihar Kaduna, ya bayyana marigayi Afaka a matsayin mutum mai gaskiya, iya aiki da rikon amana wanda ya tafiyar da aikinsa cikin matukar kulawa.

Karin bayani akan: Afaka, Shugaba Muhammadu Buhari, Saudiyya, Nigeria, da Najeriya.

Shugaban ya tuna a shekarar 2016, yayin da yake aikin hajji a Saudiyya, marigayin wanda soja ne ya tsinci wata jaka da makudan kudaden kasashen waje ya mika ta ga Hukumar aikin hajji ta kasa, matakin da ya jawo masa yabo daga hukumomin Saudiyya da na Najeriya.

Daga karshe ya kara da rokon Allah ya bai wa iyanlansa da abokansa hakurin jure rashin.

XS
SM
MD
LG