Accessibility links

An Kira Dokar Ta-Baci Da Shugaba Jonathan Ya Kafa Da Cewa "Mutm-mutumi Ne"

  • Aliyu Imam

Sojoji suke fareti a Baga.

Dokar Ta Baci nan "mutum-mutumi ne" shugaba Jonatahan ya kafa, yana ji zai yi aiki, ina ji ba zata yi aiki ba, inji Dr. Aliyu Usman Tilde.

A cikin wani sharhi da ya wallafa a dandalin Facebook, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum da Dr. Aliyu Usman Tilde, yace shugaba Jonathan ya sayi "mutum mutmi", wadda aganin shi shugaban, zai yi aiki, amma ni kuma nake gani ba zai yi tasiri ba.

Dr Tilde yaci gaba a cikin sharhin nasa, yace banbancin tsakani dokar ta baci da shugaba Jonatahan ya ayyana da wacce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa shine, sojoji ne suke da ikon tsaro a jihohin da aka kafawa dokar, yayinda 'yan siaysa da suke rike da madafun mulki zasu cigaba da yin haka, sannan za'a jingine 'yancin da 'yan kasa suke da shi cikin wadan nan jihohi.

XS
SM
MD
LG