Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Kamfanin Tuwita Ya Yi Rijista Da NBC Da CAC - Gwamnatin Najeriya


Malami & Falana

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta dage haramcin da ta yi wa kamfanin kafar sada zumunta na Tuwita, idan ya yi rijista da hukumar da ke kula da kafafen yada labarai ta NBC da hukumar CAC mai yi wa kamfanoni rijista a kasar.

A zaman sauraren bahasi kan lamarin a wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a jihar Lega, gwamanatin Najeriya ta ce ba ta hana ‘yan kasar yin amfani da dandalin sada zumunta na Tuwita din ba domin a kullum akasarin yan kasar na ci gaba da amfani da kafar duk da haramcin da ta yi.

Ministan shari’a Abubakar Malami, da gwamnatin kasar dai sun bayyana hakan ne a cikin wata takardar rashin amincewar da suka gabatar a gaban kotun don mayar da martani ga wata kara da wani lauya mai kare hakkin bil’adama mai suna, Inibehe Effiong ya gabatar.

Idan ana iya tunawa, a ranar 4 ga watan Yuni ne gwamnatin Najeriya ta haramta ayukan Tuwita a kasar a cikin kasa da sa’o’i 48 bayan shafe wani jawabi da shugaba Muhammadu Buhari ya yi kan masu tada kayar baya a kasar.

Sai dai akasarin ‘yan Najeriya sun bijirewa haramcin da gwamnatin kasar ta yi wa kafar ta Tuwita inda su ke zagayawa ta wata kafa mai zaman kanta wato VPN suna ci gaba da yin amfani da Tuwita din.

Baya ga haramta yin amfani da Tuwita da gwamnatin Najeriya ta yi, ministan shari’a Abubakar Malami, a cikin wata sanarwa ya yi gargadi kan hukunta duk dan kasar da ke ci gaba da amfani da dandalin na Tuwita.

Haka kuma hukumar da ke kula da kafafen yada labarai a Najeriya wato NBC, ta umarci dukkannin gidajen radio da talabijan a kasar su daina amfani da Tuwita ko daukan bayanai daga dandalin.

Daga bisani dai wani lauya mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Inibehe Effion, ya shigar da kara a kan ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad, da gwamnatin Najeriya a gaban kotu, sakamakon haramta kafar sada zumunta na Tuwita din.

A cikin karar da lauyan ya shigar, ya na neman samun biyan bukatu tara da suka hada da umarni na dindindin da zai hana wadanda ake kara daga ci gaba da dakatar da ayyukan dandalin Tuwita a kasar, hana ayyukan dandalin Tuwita baki daya, da ma duk wata kafar sada zumunta yin aiki a Najeriya saboda hakan ya saba wa hakkin bil’adama.

Effiong ya kuma bukaci kotu ta ayyana kalaman ministan shari’a da na watsa labarai da al’adu, na hukunta duk dan Najeriya da ya ki mutunta dokar hana amfini da tuwita a matsayin abun da ya sabawa doka sakamakon rashin hurumin doka.

A cikin wata takardar rantsuwa da Mista Ilop Lawrence ya gabatar a madadin gwamnatin Najeriya da antoni janar Malami, ya bayyana cewa dakatar da shafin na Twitter ba take hakkin bil’adama ba ne, domin har yanzu ‘yan Najeriya na amfani da Tuwita duk da haramcin da gwamnatin kasar ta yi.

Takardar rantsuwar da lauyan gwamnati ya gabatar ta bayyana cewa, lauya Effiong da ‘yan Najeriya da ya ke neman ya wakilta na iya amfani da kafar Tuwita din a duk inda su ke a fadin duniya da ma cikin Najeriya duk da haramcin da gwamnatin kasar ta yi.

Mista Ilop Lawrence ya kara da cewa, gwamnatin kasar ba ta haramta kafar Tuwita don cin zarrafin yan kasar ko kuma take hakkinsu na yancin fadin albarkacin bakinsu ba.

Haka kuma ya bayyanawa kotu cewa, ‘yan kasar na da yancin yin amfani da sauran kafafe kamar WhatsApp, Facebook, TikTok da dai sauransu kuma gwamnati ta yi watsi da batun ta na da masaniya kan goge sakon shugaba Buhari kan yakin basassar Byafara wanda aka ce sakon ne ya yi sanadin fusata yan kasar da dama.

Kazalika, gwamnatin Najeriya ta ce kafar Tuwita ta maida dandalin wajen da masu neman tada zaune tsaye kamar Nnamdi Kanu ke zuwa yin kalaman da ka iya wargaza kasa da ma marawa masu zanga-zangar EndSars baya a watan Oktobar shekarar 2020 wanda wasu miyagun iri suka juya aklarta zuwa tarzoma tare da lallata dukiyoyi da kashe mutane da ba su ji ba su gani ba.

Daga karshe, gwamnatin kasar ta ce, kamata yayi ‘yan Najeriya su nuna fushinsu kan Tuwita ba wai gwamnati ba saboda ba yadda gwamnati za ta dakatar da kamfanin Tuwita idan ya bi dokokin kasa wajen gudanar da ayukansa.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG