Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Rasha Ta Girbi Abin Da Ta Shuka - Biden


Jawabin Shugaba Biden kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:49 0:00

Jawabin Shugaba Biden kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine

Putin ne ya zabi shiga wannan yaki da kansa, saboda haka, shi da kasarsa za su girbi abin da suka shuka. Biden ya ce.

Shugaban Amurka Joe Biden, ya sanar da saka wasu sabbin takunkumi akan Rasha, bayan mamayar da Shugaba Vladimir Putin ya kai da sanyin safiyar jiya Alhamis akan Ukraine din da ke makwabtaka da Rashar.

Biden ya sanar da daukan wannan mataki ne yayin wani jawabi da ya yi wa Amurka kan abin da ke faruwa a Ukraine.

“Putin ne ya zabi shiga wannan yaki da kansa, saboda haka, shi da kasarsa za su girbi abin da suka shuka. A yau ina mai sanar da karin takunkumai masu tsauri, tare da takaita abin da za a iya kai wa Rasha, hakan zai haifar da mummunan tasiri akan tattalin arzikin Rasha a yanzu da kuma nan gaba.

“Muna sane muka tsara wadannan takunkumai, don su takura Rasha na wani tsawon lokaci, ta yadda a gefe guda kuma ba za su tsawwalawa Amurka da kawayenmu ba.” In ji Biden.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Wadannan sabbin takunkumi sun hada da wasu bankunan Rashar, da wasu mashahuran mutane da kuma wasu bangarorin da suka shafi ayyukan samar da fasahohin zamani.

Ko da yake, Shugaba Biden ya ce Amurkawa za su dan ji hucin wannan takunkumi a fannin sayen man fetur, saboda farashinsa da ya tashi a kasuwar duniya sanadiyyar mamayar da Rashar ta yi wa Ukraine, amma ya kara da cewa, “bai kamata wannan takalar fada da Rashar ta yi a bar ta tafi salum-alun ba, domin a ko da yaushe, Amurka na goyon bayan ‘yancin walwala ne.

Sai dai Biden ya ce, gwamnatinsa ba ta da shirin tura dakarun kasar zuwa cikin Ukraine, amma kuma ya yi alkawarin cewa, dakarun na Amurkar za su marawa sojojin NATO baya, idan har mamayar ta Putin ta wuce Ukraine, ta hada da daya daga cikin mambobin kungiyar tsaro NATO 30.

Wani yanki da aka kai hari a Ukraine
Wani yanki da aka kai hari a Ukraine

“Na ba da umarnin tura karin dakaru zuwa Jamus, a wani mataki da NATO ke shirin dauka, ciki har da wasu dakarun Amurkar da hukumar tsaron kasar ta saka su cikin shirin kar ta kwana a ‘yan makonnin da suka shude”

Shugaba Biden ya kara da cewa, akwai yiwuwar matakin da za su dauka nan gaba, zai hada har da saka takunkumi akan kadarorin Putin, idan har mamayar da Rashar ta yi wa Ukraine ta fadada.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis Putin ya kai mamaya cikin kasar ta Ukraine, lamarin da rabon da a ga irinsa, tun karshen yakin duniya na biyu, inda dakarun Rashar suka far wa na Ukraine a gabashin kasar da ake takaddama da kuma wasu muhimman biranen kasar ciki har Kyiv, babban Birnin kasar

Shi dai Putin ya ayyana lamarin a matsayin matakin kwance damarar Ukraine, wacce a da ta kasance mamba a tsohuwar tarayyar Soviet, amma ta samu ‘yanci tun a shekarar 1991.

Matakin dai ya janyo kakkausar suka daga sassan na duniya inda Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar tarayyar turai da wasu shugabannin duniya masu fada a ji, suka yi tir da lamarin.

XS
SM
MD
LG