Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Cika Shekaru 8 Da Sace 'Yan Matan Chibok-Kashi Na Daya-Afrilu, 14, 2022


Alheri Grace Abdu

Yau shirin Domin Iyali ya tattauna kan batun sace ‘yammatan Chibok da aka cika shekaru takwas cif yau, da bayanai ke nuni da cewa, har yanzu ba a san yanayin da dari da goma daga cikin dalibai 276 da aka sace su ke ciki ba.

Wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda ta tattauna da shugaban ‘yan asalin Chibok mazauna birnin tarayya Abuja Nkeki Mutah, da Madam Martha Bitrus Dalu ita ma ‘yar asalin Chibok wadda kuma ta rubuta littafi kan sace ‘yan matan.

Saurari kashin farko na tattaunawar:

DOMIN IYALI: Cika Shekaru 8 Da Sace 'Yammatan Chibok-Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:09 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG