Accessibility links

Dubban Mutane Sun yi Gudun Hijira Zuwa Adamawa


Gawarwakin mutanen da 'Yan Boko Haram suka kashe a Konduga, Jihar Borno, Fabrairu 12, 2014.

Fiye da mutane dubu 10 suka arce zuwa cikin jihar Adamawa a bayan da 'yan bidniga suka sake kai farmaki a kan kauyen Izghe dake bakin iyaka a Jihar Borno

Dubban mutane su na ta arcewa daga Izghe da wasu kauyukan dake kusa da nan a bakin iyakar Borno da Adamawa, a bayan wani kazamin harin ta'addancin da aka kai aka kashe mutane masu yawa a kauyen.

Malam Madu Dauda, wanda ya gudu zuwa Yola, babban birnin Jihar Taraba daga kauyen na Izghe, yace kafin ya bar garin sai da suka yi sallar gawarwaki fiye da sittin. Yace an kona kusan dukkan gidajen dake wannan kauyen.

Hukumomin soja, sun roki jama'a da su rika ba su labari cikin gaggawa na duk wani abinda ba su yarda da shi ba domin su samu sukunin kai musu taimako da wuri, ganin cewa ba za a iya girka sojoji a kowane gari da kauye dake nan ba.

XS
SM
MD
LG