Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubun Wasu 'Yan Bindiga Ta Cika Yayin Da Suke Karbar Kudin Fansa


Gunmen
Gunmen

Wasu gaggan ‘yan bindiga sun gamu da ajalinsu, a yayin karbar kudin fansar wani da suka sace a jihar Taraba.

Lamarin ya auku ne bayan da ‘yan bindigar suka sace wani dattijo, Alhaji Gambo, a garin Sabongida da ke cikin karamar hukumar mulkin Gassol ta jihar Taraba.

Rahotanni sun bayyana cewa jagororin ‘yan bindigar da suka sace Alhaji gambo, da aka bayyana su da sunan Sani da Musa, sun tuntubi iyalansu suka nemi a biya kudin fansa.

Bayan cimma matsaya akan adadin kudaden sai kuma aka shaidawa iyalan inda za su kai kudin domin su karbi dattijon.

To sai ‘yan banga da ‘yan sa kai da suka sami labarin, sun shirya tare da yi kwanton bauna a wurin da aka shata karbar kudin.

Su kuwa ‘yan bindigar biyu, Sani da Musa, duk da yake suna rike da muggan makamai, to amma ba su da masaniya akan cewa ‘yan sa kai sun zagayen wajen a kwance cikin shiri, ai kuwa sai kawai suka ji ruwan harsasai da isarsu a wurin da aka shata.

Nan take kuwa aka sami harbe ‘yan bindigar biyu a lokacin da suke kokarin karbar kudin fansar, yayin da shi kuma dattijon da suka sace Alhaji Gambo, aka sami kubutar da shi zuwa gida.

Wata majiya ta fadawa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindigar da aka kashe, sun dade suna addabar jama’a.

Majiyar ta ce Sani da Musa sun yi suna sosai a kai hare-hare da kashe mutane da dama a garuruwan Borno-Korokoro, Tella, Sabongida, Dananacha da sauran makwabtan kauyuka da ke kan babban titin Jalingo zuwa Wukari a jihar ta Taraba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ASP Abdullahi Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Halin la-haula da yanayin tsaro ya shiga a Najeriya dai ya haifar da daukar matakai daban-daban daga bangaren al’umma domin kare kan su, a yayin da masu fashin da dama suke bayyana korafin cewa hukumomin tsaron kasar sun kasa a yaki da ‘yan ta’adda.

To sai dai sau tari hukumomin tsaron kan musanta ikirarin, inda suke cewa suna iya kokarinsu, wasu lokutan ma har da ba da bayani da kuma lokacin da suke hasashen kai karshen matsalar tsaron.

XS
SM
MD
LG