Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DUNIYAR AMURKA: Tattaunawa Kan Takaddamar Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, 06 Janairu, 2023


Mahmud Lalo
Mahmud Lalo

To shin me ya sa ‘yan majalisar suka gaza zaben Kakakinsu, ko mene ne korafin ‘yan Republican da suka ki zabar dan jam’iyyarsu? Kadan kenan daga cikin abubuwan da muka tattauna tare da mai fashin baki Dr Nasir Danmowa.

Kwana uku bayan da suka hallara a zauren majalisar dokokin Amurka, sabbin ‘yan majalisar wakilan kasar sun gaza zabar kakakin majalisar saboda cijewa da wasu ‘yan Republican suka yi na kin zabar Kevin McCarthy a matsayin kakakin majalisar wacce ‘yan Republican suka karbe rinjayenta daga hannun ‘yan democrat bayan zaben rabin wa’adi da aka a watan Nuwambar Bara.

DUNIYAR AMURKA: Tattaunawa Kan Takaddamar Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka - 8'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:08:52 0:00

XS
SM
MD
LG