Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola ta Bulla a Kasar Mali


Wani ma'aikacin kula da lafiya a kan iyakar kasar Mali ya na auna zafi jikin masu shiga kasar daga Guinea

Wata yarinya 'yar shekaru biyu ce ta fara mutuwa a kasar ta Mali da cutar Ebola.

Jami'an kula da lafiya a kasar Mali sun ce wata yarinya 'yar shekaru biyu wadda kwanan nan aka je da ita kasar Ghana, ta mutu sanadiyar cutar Ebola.

Yarinyar da ta mutu jiya Jumma'a, ita ce ta farin farkon da aka tabbatar da mutuwar ta sanadiyar Ebola a kasar Mali.

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce yarinyar da iyayen ta sun yi cudanya da mutane da dama a cikin bas din da suka yi balaguron, kuma Hukumar ta yi kashedin cewa mutane da yawa na iya fadawa cikin kasadar kamuwa da cutar.

Majiyoyin ofisoshin jakadancin kasashen wajen da ke kasar Mali sun bayyana damuwa game da ko gwamnatin kasar ta Mali na cikin shirin iya tinkarar cutar. Mali dai na cikin kasashen duniya mafiya talauci.

Yanzu haka dai barkewar cutar Ebola ta fi yawa a kasashen Yammacin Afirka uku, wato Guinea da Laberiya da kuma Saliyo. Ta hallaka mutane kusan dubu biyar (5,000) daga cikin sama da dubu goman (10,000) da aka san sun kamu da ita. An samu bullar cutar jefi-jefi a Turai da kuma nan Amurka.

A jiya Jumma'a Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce ta na shirin samar da dubban daruruwan alluran cutar Ebola nan da zuwa tsakiyar shekarar dubu biyu da goma sha biyar (2015).

A jiya Jumma'a shugabannin kungiyar Tarayyar Turai suka yi sanarwar cewa sun ware dola miliyan dubu daya da miliyan dari ishirin da biyar domin taimakawa a yakin da ake yi da matsalar Ebola a yankin Yammacin Afirka.

A wani nlabarin kuma, ma'aikatan jinyar Amurka biyu da suka kamu da cutar Ebola lokacin da suka kula da wani dan kasar Laberiya mai cutar a Dallas, jahar Texas, sun warke, yanzu ba sa dauke da kwayar cutar.

Shugaba Barack Obama ya na ganawa da ma'aikaciyar jinya Nina Pham a fadar shi ta White House bayan an tabbatar da cewa ta rabu da cutar Ebola
Shugaba Barack Obama ya na ganawa da ma'aikaciyar jinya Nina Pham a fadar shi ta White House bayan an tabbatar da cewa ta rabu da cutar Ebola

A halin da ake ciki kuma wani ba'amurken da ya kamu da cutar Ebola ya sa an dauki sabbin matakan sa mutane zaman kulle a killace a cikin New York da kewaye. Dr.Craig Spencer wanda kwanan nan ya koma New York daga kasar Guinea inda yayi jinyar masu cutar Ebola, shi ma a ranar Alhamis aka tabbatar da cewa ya kamu da cutar.

Gwamnan Jahar New York Andrew Cuomo da na jahar New Jersey Chris Christie sun fada a jiya Jumma'a cewa duk wanda zai shiga jahohin su bayan yayi cudanya da masu cutar Ebola a Yammacin Afirka, zai yi kwanaki 21 cikin zaman kullen dole a killace.

Tuni dai har an sanya wata mata cikin wannan hali na kullen kwanaki 21 na dole a killace daga saukar ta jiya Jumma'a a babban filin jiragen saman Liberty na Newark a jahar New Jersey.

A cikin jawabin shi na sati-sati ga 'yan kasa,shugaba Barack Obama ya yiwa Amurkawa kaimi da kiran cewa su yi aiki da sani na ilimin kimiyya game da yaki da cutar Ebola. Ya ce kamata yayi mu bi yadda kimiyya ta zo ma na da bayani, amma kar mu bari tsoro ya kama mu.

XS
SM
MD
LG