Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebrahim Raisi Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Iran


Ebrahim Raisi
Ebrahim Raisi

Tsohon shugaban babban bankin kasar Abdolnasser Hemmati, wanda ya yi takara da Raisi ya amince da shan kaye.

Ebrahim Raisi mai tsananin ra’ayin mazan jiya ya lashe zaben shugaban kasar Iran.

A ranar Juma’a Iraniyawa suka kada kuri’unsu a zaben shugaban kasar wanda tun da farko aka yi hasashen Raisi ne zai lashe.

An ruwaito yiwuwar samun karancin masu zuwa kada kuri’a tun gabanin zaben, sanadiyyar kiran da ‘yan adawa suka yi na a kaurcewa zaben.

Majalisar kolin kasar da ke tantance ‘yan takara ta bar Raisi da wasu ‘yan takara shida ne kawai suka kara a zaben bayan da ta soke takarar fitattun ‘yan siyasa da dama da suka nuna sha’awarsu ta shugaban kasar, wacce ke karkashin takunkumai da dama.

Tsohon shugaban babban bankin kasar Abdolnasser Hemmati, wanda ya yi takara da Raisi ya amince da shan kayi.

“Ina fata gwamnatinka, karkashin jagorancin shugaban addini Ayatollah Ali Khamenie, za ta kawo ci gaba ga kasarmu.” Hemmati ya fada a wata sanarwa kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

XS
SM
MD
LG