Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Yi Kunnen Doki Da Everton, Solskjaer Ya Ajiye Ronaldo A Benci


Ronaldo da 'yan wasan Everton a tsaitsaye
Ronaldo da 'yan wasan Everton a tsaitsaye

Manchester United ta raba maki da Everton a wasan da suka buga bayan da aka tashi da ci 1-1 a gasar Premier League ta Ingila.

United ce ta fara zura kwallo a ragar Everton ta hannun Antony Martial ana shirin tafiyar hutun rabin lokaci.

Sai dai Andres Townsend ya farke kwallon a minti na 65.

Everton ta so ta kwashe duka maki ukun wasan, amma alkalin wasa ya soke kwallon da Yerry Mina ya buga ta wuce David de Gea, bayan da na’urar VAR ta tabbatar ya yi satan gida.

Lokacin da Everton ta farke kwallon, an sako Cristiano Ronaldo a wasan wanda ya shigo daga benci.

Sai dai a wannan karon, Ronaldo bai yi nasarar kwato United a filin na Old Trafford ba.

A wasan Champions League da aka buga, Ronaldo ya ceto United a hannun Villareal, inda ya ci kwallon da ta ba su nasara da ci 2-1 a gasar.

Ya ci kwallon ne a cikin karin lokacin da aka yi a wasan.

Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?

Ole Gunnar Solskjaer
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG