Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Erdogan Yaki Amincewa Da Bukatar Amurka


Shugaba Erdogan na Turkiya
Shugaba Erdogan na Turkiya

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya mayarwa mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin waje John Bolton martani kan bukatar sai Turkiyya ta tabbatar da cewa bazata kaiwa mayakan Kurdawa dake Arewa maso gabashin Syria hari ba, kafin Amurka ta janye sojojinta daga kasar.

Shugaba Erdogan ya yi wannan kalaman ne ya yin da Bolton ya kai ziyara Ankara domin tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar. Erdogan ya soke ganawar da aka shirya zai yi da Bolton, maimakon haka sai Bolton ya gana da wasu jami’an gwamnati ciki har da mai magana da yawun shugaban kasa da kuma ministan tsaron Turkiyya.

Da yake magana gaban mambobin jam’iyyarsa ta AK, da kakkausar muryar Erdogan ya yi watsi da maganar Bolton, yana mai cewa Turkiyya ba zata amince yin sulhu ba, yana mai danganta kurdawan da sauran kungiyoyin ta’addanci a Syria.

Shugaba Erdogan ya ce, “Akan wannan batu, John Bolton ya tafka babban kuskure, kuma duk wanda yake tunani irin wannan shima yayi kuskure. Ba abu ne mai yiwuwa a wannan lokaci mu amince da wani sulhu ba. Duk wadanda ke cikin ‘yan ta’adda a Syria za su fuskanci darasin da ya dace da su. Babu wani banbanci tsakanin ‘yan kungiyar PKK da YPG da PYD da kuma Daesh.”

Bolton dai bai sami hadin kai ba a kokarin da ya shafe sa’o’i biyu domin neman sasantawa don kare Kurdawan da Amurka ke marawa baya a Arewa maso gabashin Syria.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG