Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Tace Zata Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka


Masu tattaunawar Taliban

Kungiyar Taliban tace tattaunawarta da Amurka a kan kawo karshen yaki da wasu ayyukan da basu dace ba a Afghanistan tana nan yadda take amma kuma taki yarda da shiga wata tattunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar kai tsaye a Kabul.

Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya fadawa Muryar Amurka cewa akwai wata tattaunawa da kungiyar zata yi da Amurka amma dai ba a fitar da rana da kuma inda za a yi tattaunawar ba.

Mujahid yana mai da martani ne tare da watsi da rahotanni da ya kira na karya, cewa wakilan kugniyar mayakan sa kan suna shirin shiga wata tattaunawa da jami’an Afghanistan a Saudi Arabia a wata mai zuwa.

Wakilin Amurka na musamman mai shiga tsakani a Afghanistan, Zalmay Khalizad ya yi wata tattaunawa ta lokaci mai tsawo tsakanin kwanaki biyu a tsakiyar watan Disemba da wata babbar tawagar Taliban a birnin Abu Dabi, inda wakilan Saudi Arabi da na Pakistan da ma na kasar dake daukar nauyin tattaunawar suka halarta.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG