Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Tace Ba A Kai Ga Musayar Ba-Amurken Nan Whelan Da Maria Ba


Whelan dan Amurka da Rasha ta kama

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha a jiya Asabar ya yi watsi da batun yiwuwar yin musayar ba-Amurken nan da ake tsare da shi bisa zargin leken asiri da wata ‘yar kasar Rasha.

An tsare Paul Whelan tsohon sojan ruwan Amurka dan asalin kasashen Birtaniya da Ireland ne a karshen watan Disemba a Moscow. Kama shi ya haifar da tsegumin cewa Rasha tana so ta yi amfani da shi domin tayi musaya da wata ‘yar kasarta da ta aikata laifin leken asiri a Amurka.

Amma mataimakin na ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya fada cewa lokacin tattaunawa a kan yiwuwar musayar Whelan da Maria Butina bai kai ba, saboda ba a riga an tabbatar da laifi a kan Whelan a hukumance ba, a cewar kamfanin dillancin labaran Rasha.

Tun da farko wasu kafafen yada labarai a Rasha sun ce wata majiya da basu bayyana ba tace akwai yiwuwar tabbatar da lafin leken asiri a kan Whelan, lamarin da ka iya kai shi gidan yari tsawon shekaru 20.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG