Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ba Zata Nuna Hotunan Gawar Osama bin Laden ba


Shugaban Amurka Barack Obama a ofishin shugaban amurka da ake kira Oval Office.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yanke shawarar ba zai saki hotunan da suka nuna gawar Osama bin Laden ba.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yanke shawarar ba zai saki hotunan da suka nuna gawar Osama bin Laden ba,da sojojin kundunbalan Amurka suka dauka bayan an kasheshi ranar litinin.

Kakakin fadar White House Jay Carney ya fada laraban nan cewa,shugaban kasan ya yanke shawarar cewa sakin hotunan bashi da wani fa’ida.Yace saboda munin hotunan,sakinsu zai yi barazana ga tsaron Amurka,kuma hakan yana hura wutar fitina.

Shugaban na Amurka ya bayyana shawarar da yanke ne lokacin da yake hira cikin shirin tashar talabijin ta CBS. Mr. Obama yace bashi da wani kokonto cewa sojojin Amurka sun kashe bin Laden. Yace mutuminda ya kasance kanwa uwar gamin harin d a aka kawowa Amurka ranar 11 ga watan Satumban 2001,ya sami hukunci da ya dace.

Carney ya fada laraba cewa galibin masu baiwa shugaban Obama shawara sunce a ci gaba da sirranta hotunan. Yace ko wani bangare yana hujjojin neman a bayyana hitunan,da kuma wadanda basu goyi bayan haka ba.

Kakakin fadar shugaban kasan ya sake jaddada ikirarin da Atoni Janar na Amurka Eric Holder ya yai cewa farmakin da Amurka ta kai da ya halaka shugaban na al-Qaida bai sabawa doka ba.

Yace sojojin kundunbalan Amurka na musamman din, a shirye suke su kama Osama bin Laden,day a mika wuya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG