Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewa A Mahakar Gawayin Coal A China Tayi Sanadin Bata Da Rayukan Ma'aikata


Ma'aikatan ceto

Akalla mutane 13 sun mutu wasu su 20 kuma sun bata bayan wata fashewa da ta auku a wata mahakar gawayin Coal dake yankin Chongqing na kasar China.

Fashewar ta faru ne a wata mahaka mai zaman kanta dake garin Laisu da safiyar jiya litinin, a cewar kamfanin dillancin labaran Xinhua.
Mataimakin magajin garin Chongqing ya fadi cewa an kaddamar da shirin neman mahakan da suka bata, ko da yake kokarin aikin ceton na fuskantar cikas saboda baruguzan da fashewar ta haddasa da kuma ganin iskar gas ta gurbata wurin da guba.
Hukumomi sun riga sun kaddamar da bincike akan mummunar fashewar kuma jami’an yankin sun bada umurnin dakatar da aiki a kananan mahakun dake yankin na dan lokaci.
A farkon shekarar nan, kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ce hukumar kula da harkokin magashin kasar China ta ce, an sami hadarurrukan gas guda 171 a mahakun kwal guda 45 a shekarar da ta gabata.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG