Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Wani Abu Mai Kamar Bam Ta Raunatu Yara 7 a Jihar Kaduna


A daidai lokacin da ake fama da matsalar tsaro a wasu yankunan jihar Kaduna, wani abun fashewa ya tarwatse inda ya jikkata yara bakwai a Anguwar Mangwaro da ke karamar hukumar Igabi.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar a yammachin jiya Talata, ta ce wasu yara ne su ka tsinto wasu abubuwa inda a garin wasa su ka fashe har su ka jikkata yara bakwai. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya yi wa Muryar Amurka karin bayani ya na mai cewa abin da ya fashe ba bam bane, amma wani abu me mai kama da nakiya.

Kwamishainan ya kara da cewa, yaran su bakawai suna nan a asibiti inda ake jinyarsu kuma ana samun biyan bukata.

Wani mutum Alh. Dayyabu Kerawa daya daga cikin kansilolin Karamar hukumar Igabi kuma abokin mahaifin yaran da wannan fashewa ta shafa ya ce abun ya zo da sauki.

To shin ko dama jami'an tsaro kan zubar da irin wadannan abubuwa masu fashewa? Wannan ce tambayar da muka yi wa masanin harkokin tsaro, Manjo Mohammed Bashir Shu'aibu Galma mai ritaya inda ya ce ba haka ba ne, amma gwamnan ya sa ayi bincike kuma suna kokarin dubawa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka sami irin wannan fashewa cikin 'yan kwanakin nan ba, Domin kuwa a jihar Zamfara ma an sami fashewar da ta yi sanadin kashe wasu yara.

Saurari rahoton cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:

Fashewar Wani Abu Mai Kamar Bam Ta Raunatu Yara 7 a Jihar Kaduna
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00


Karin bayani akan: Jihar Kaduna, harin bam, Nigeria, da Najeriya.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG