Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an kwantar da tarzoma sun kaiwa masu zanga zanga hari a Bahrain


Masu zanga zanga a Bahrain

Babbar jam’iyar hamayya a Bahrain tace an kashe a kalla masu zanga zanga biyu da asubahin yau alhamis

Babbar jam’iyar hamayya a Bahrain tace an kashe a kalla masu zanga zanga biyu da asubahin yau alhamis yayinda ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka kutsa babban dandalin dake Manama babban birnin kasar, suna korar dubban masu zanga zangar da suka kafa sansanoni a wruin suna neman a yi gagarumin garambawul a harkokin siyasar masarautar dake tsibiri. Kafin wayewar gari, yau, dandalin ya yi wayam banda mutane kalilan da jami’an ‘yan sanda suke yiwa tambayoyi. Jami’an tsaro sun kutsa dandalin Pearl kafin wayewar garin yau alhamis, suna kaiwa masu zanga zangar da suka mamaye wurin na tsawon kwanaki uku hari. Babu tabbacin ko akwai wadanda suka jikkata. Zuwa faduwar rana, masu zanga zangar wadanda akasari ‘yan shi’a ne, sun yi tururuwa a Pearl Square bayan zanga zangar ruwan sanyi ta kwana daya. Tun farko daruruwan mutane sun shiga sahun masu zanga zangar wajen makokin masu zanga zanga biyu da aka kashe tunda aka fara zanga zangar ranar Litinin. Shugabannin hamayya na ‘yan Shi’a sun bayyana cewa, basu sha’awar ganin masarautar ta rikide ta kama salon mulkin kama karya irin na kasar Iran. Mujallar World Street Journal ta laburta cewa, kungiyoyin hamayya guda biyar da suka hada da fitattar jam’iyar Wafaq sun sanar da kafa kwamiti da zai taimaka wajen tsara zanga zangar da kuma gabatar da bukatar ta bai daya. Muhajjar tace kwamitin yana shirin gudanar da gagarumar zanga zanga ranar asabar

XS
SM
MD
LG