Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fursunoni Sama Da 3000 Ne Suka Gudu A Najeriya - Ministan Cikin Gida


Ministan cikin gida Rauf Aregbesola sanye da fararen kaya (Facebook/Ma'aikatar Cikin gida Najeriya)
Ministan cikin gida Rauf Aregbesola sanye da fararen kaya (Facebook/Ma'aikatar Cikin gida Najeriya)

Sai dai ministan ya ce suna da bayanan yatsun dukkan fursunonin kasar, fasahar da ya ce yana fatan za ta taimaka wajen kama fursunonin.

Fursunoni dubu 3,876 ne suka tsere daga gidajen yari daban-daban a sassan Najeriya a tsakanin shekarar 2020 zuwa wannan shekara, in ji ministan cikin gida Rauf Aregbesola.

Lokaci na baya-bayan nan da fursunoni suka gudu shi ne a jihar Oyo inda kusan mutum 1000 suka tsere bayan da wasu ‘yan bindiga suka fasa gidan yarin Abolongo.

Koda yake hukumomi sun ce sun kama kusan 400 daga cikinsu.

Yayin da yake magana da manema labarai a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja a ranar Alhamis, Aregbesola ya ce adadin fursunonin da suka gudu a sassan kasar a tsakanin 2020 zuwa 2021, sun kai 4,860 amma an kama 984.

Hakan na nufin fursunoni 3,876 na nan a cikin jama’a.

Sai dai ministan ya ce suna da bayanan yatsun dukkan fursunonin kasar, fasahar da ya ce yana fatan za ta taimaka wajen kama fursunonin.

A watan Afrilu wasu ‘yan bindiga suka fasa gidan yari a birnin Owerri da ke jihar Imo a kudu maso gabashin kasar, suka kubutar da fursunoni sama da 1,800.

A wata hira da ya yi da manema labarai a farkon shekarar nan, ministan cikin gidan ya ce duk fursunan da ya mika kansa bisa ra’ayinsa ba zai fuskanci wata tuhuma ba.

Sai dai a akwai lokuta da dama da duk da fasa gidajen yarin da ake yi a sassan kasar, akan samu wasu daga cikin fursunonin da kan ki guduwa.

XS
SM
MD
LG