Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Sun Zargi Gwamnati Da Tabarbarewar Tsaro


Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya

A Najeriya bisa ga yadda lamarin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a yankin Arewa da kuma kasawar gwamnatin kasar wajen magance matsalar ya sa gamayyar kungiyoyin Arewa ta dora alhakin faruwar matsalolin kan gwamnatin kasar.

Kungiyar ta kuma daura damarar daukar matakan da suke fatar zasu samar da mafita daga wadannan matsalolin a lokacin da kungiyoyin suka hadu a Sakkwato dake Arewa maso Yammacin kasar domin daukar matakan.

Lamarin rashin tsaro a Arewacin Najeriya yana ci gaba da karuwa musamman a Jihohin Arewa maso Yamma inda abin har ya kai ga kona mutane da rayukan su har su mutu wanda a kullum kokawa suke yi.

Game da yadda lamarin ke ci gaba da wanzuwa kuma har yanzu matakan da mahukunta ke dauka sun kasa warware matsalolin musamman kisan gilla ga matafiya a Sakkwato yasa gamayyar kungiyoyin ta Arewa suka hadu a jihar don duba yadda zasu fitowa lamarin.

Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin Arewa Nastura Ashir Shariff ya ce sun fara ne da zaman tattaunawa da wadanda lamarin ya shafa kai tsaye kuma daga cikin abubuwan da suka gano akwai kasawar hukuma tamkar babu gwamnati a kasa. Hakama sun lura da cewa jagororin Arewa basu damu da ganin ci gaban ta ba.

Daidai lokacin da gamayyar kungiyoyin na Arewa ke wannan shirin, tuni wasu jama'a su ka dukufa ga addu'o'i yayinda ita kuwa hukuma ke cewa tana ta kokari duk domin a samu kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Sun Zargi Gwamnati Da Tabarbarewar Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00


An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG