Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gareth Bale Na Ban-Kwana Da Real Madrid


Gareth Bale
Gareth Bale

Bale ya taimakawa Real Madrid ta lashe kofi 19, ciki har da na nahiyar turai guda biyar, inda ya zura kwallaye a shekarar 2014 da 2018 a gasar Champions League.

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale ya tabbatar ranar Laraba cewa zai bar kungiyar, yana mai cewa burinsa ya cika na taka leda tare da zakarun nahiyar turai.

Bale, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen wannan wata na Yuni, ya koma Real Madrid ne a shekarar 2013 daga Tottenham ta Ingila, wacce ya bugawa wasa a matsayin dan wasan aro.

“Kasancewa dan wasa a wannan kungiya tare da cin ma burin abin da muka saka a gaba yayin da nake Real Madrid, ya zama min abin alfahari da ba zan taba mantawa ba.” Bale ya ce cikin wata wasika da ya rubuta ta ban kwana kamar yadda AP ya ruwaito.

Bale ya taimakawa Real Madrid ta lashe kofi 19, ciki har da na nahiyar turai guda biyar, inda ya zura kwallaye a shekarar 2014 da 2018 a gasar Champions League.

Ya kuma taimakawa Madrid ta lashe kofi uku na gasar La Liga.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG