Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gareth Bale Ya Koma Tottenham


Gareth Bale

Shahararren dan wasan kungiyar Real Madrid ta kasar Spain Gareth Bale ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Tottenham da ke Ingila, a zaman aro na tsawon shekara daya.

Bale mai shekaru 31, ya bar Tottenham ne a shekara ta 2013, a kwantaragi mafi tsada a wannan lokacin na fam miliyan 85.

Tun can farko ya koma Tottenham din ne daga Southampton a shekara ta 2007, a lokacin yana dan shekara 17, akan kudi fam miliyan 5.

Bale ya zura kwallaye fiye da dari daya a zamansa kungiyar Real Madrid, inda ya lashe gasar zakarun Turai har sau 4. Haka kuma ya lashe gasar La Liga 2, Copa del Ray 1 da UEFA Super Cup 3.

Gareth Bale
Gareth Bale

Ana ganin tafiyar ta Bale tana da nasaba da tabarbarewar dangantaka tsakaninsa da kocin Real din Zinadine Zidane, duk da yake kocin ya yi ta nanata cewa ba wata tankiya tsakaninsa da dan wasan.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane

Ko baya ga Bale, Tottenham din ta kuma sayi wani dan wasan Real Madrid Sergio Reguilon a kwantaragin shekaru 5.

Dan wasan dan kasar Spain mai shekaru 23, yayi zaman aro ne a kungiyar Sevilla a kakar wasanni da ta gabata.

Facebook Forum

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG