Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Chelsea Ta Doke Manchester City


Frank Lampard na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea yana murnar jefa kwallo na biyu da yayi a ragar 'yan Manchester City ranar lahadi 12 Disamba, 2011 a filin wasa na Stamford Bridge. Chelsea ita ce kungiyar farko da ta doke Manchester City tun da aka fara

Chelsea ta yi abinda Manchester United da Tottenham suka kasa yi: ta doke Manchester City a karon farko tun da aka fara wasannin Premier League na wannan kakar kwallo

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta jijjiga rukunin Premier League na Ingila jiya lahadi a lokacin da ta doke kungiyar da tun farko ta ke kan gaba a rukunin, Manchester City, da ci 2 da 1 a karawar da suka yi a filin wasa na Stanford Bridge.

Da farkon wasa dai, an dauka cewa Manchester City zata yi kaca-kaca da 'yan wasan Chelsea, domin a can baya idan an tuna, ta doke Manchester United da ci 6 da 1, ta doke Tottenham da ci 5 da 1. Minti biyu kacal da fara wasan na jiya, sai Mario Balotelli dan kasar Italiya ya jefa ma Manchester City kwallo a ragar 'yan chelsea.

Kuma tun daga nan 'yan Manchester City suka mamaye fili su na kai kora, dama da hagu. Wasu ma sun koka cewa alkalin wasa ya hana Manchester City jefa kwallo na biyu a lokacin da aka ga dan wasan Chelsea Jose Bosingwa yayi keta ma david silva.

A minti na 34 da fara wasa, Raul Meireles dan kasar Portugal ya rama wa Chelsea kwallon, yayin da 'yan wasan Chelsea suka dauki matakan tsuke tsakiyar fili domin kawo karshen farmakin wasu 'yan wasan Manchester City su biyu da suka hana su sakat: Yaya Toure da David Silva.

Filin ya kara yin duhu ma 'yan wasan Manchester City a bayan da aka kori dan wasansu Gael Clichy, suka zamo saura 10 a fili. Manajan City, Roberto Mancini, yace "Ba mu jefa kwallayen da ya kamata mu jefa kafin a tafi hutun rabin lokaci ba, sannan wasan ya canja a bayan da aka kori Gael."

Alkalin wasa yana bayar da jan kati na kora daga fili ga dan wasan Manchester City, Gael Clichy, a minti na 58 da fara wasa, a bayan da Clichy yayi keta ma dan wasan Chelsea mai suna Ramires
Alkalin wasa yana bayar da jan kati na kora daga fili ga dan wasan Manchester City, Gael Clichy, a minti na 58 da fara wasa, a bayan da Clichy yayi keta ma dan wasan Chelsea mai suna Ramires

Manchester City ta yi kokarin kare maki akalla guda a wasan, ta hanyar canja Aguero, wanda saura kadan ya jefa kwallo na biyu a minti na 11 da fara wasa, da kuma Silva, amma kuma sai Lescott ya dama musu lissafi lokacin da ya kama kwallo da hannu yana kokarin tare wanda Sturridge ya buga. Alkalin wasa ya bada bugun fenariti.

Chelsea ta zabi Frank lampard, wanda ya shigo daga baya domin buga fenaritin, kuma daga nan kusan wasa ya kare.

A yanzu dai, maki biyu kawai Manchester City ta ba Manchester United a rukunin na Premier League. Chelsea da Tottenham su na da maki daidai, yayin da Arsenal ta ke ta biyar, maki biyu a bayan Chelsea da Tottenham. Watau duka-duka dai, maki 9 ya raba tsakanin kungiyoyi biyar dake sama a rukunin Premier League.

Sai dai kuma mutane da yawa su na ganin cewa duk da wannan kashi na farko da ta sha, kungiyar Manchester City da 'yan wasa masu tsada da ta tattara su ne ake kyautata zaton zasu iya shan ruwa zuwa karshe.

Amma dai Hausawa sun ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Manajan 'yan Chelsea, Andre Villas-Boas, cewa yayi, "maki bakwai ya raba mu da 'yan City, kuma ganin cewa akwai kungiyoyi da dama dake hankoron zamowa zakarun Premier League, maki bakwai ba wani abu ba ne."

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG