Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gawar Marigayi John Lewis Ta Isa Majalisar Dokokin Jihar Alabama


An ajiye gawar marigayi John Lewis, dan majalisar wakilan Amurka kuma shahararren dan rajin kare ‘yancin 'yan kasa na bai daya a majalisar dokokin jihar Alabama, inda jama'ar jihar tasa ta asali zasu samu damar yi ma shi karramawar karshe.

Lewis ya rasu sanadiyyar cutar sankara a makon da ya gabata ya na da shekaru tamanin a duniya bayan ya kwashe shekara guda yana fama da wani nau'in sankaran ciki.

Gawar Lewis ta isa ginin majalisar dokokin jihar Alaba a birnin Montgomery jim kadan bayan da wani keken dawaki dauke da akwatin gawarsa da aka lullube da tutur Amurka ya bi da shi ta gadar Edmund Pettis a Selma, gadar da ‘yan sanda suka taba lakada masa duka tare da wasu ‘yan fafutukar neman ‘yancin 'yan kasa na bai daya da suka yi tattaki, suka yi kokarin tsallaka gadar zuwa Montgomery a shekarar 1965.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG