Mataimakin shugaban kasa Mike Pence, wanda shi dan wani tsohon sojan yakin Korea ne, zai halarci buki na biyu idan gawarwakin suka iso barikin sojan Amurka dake Hawaii.
A wurin bukin tahowa da gawarwakin da aka gudanar a filin saukar jirage sojoji na Korea ta Arewa, kwamandan dakarun Amurka a yankin Korea, ya yi tsokaci kan muhimmancin dawowa da wadanda suka mutu a fagen daga da kuma fursinonin yaki.
Yace ga jarumi, wannan wani aiki ne da ya dace kuma alkawari ne da yake dauka kafin ya je fagen daga kana hakan na ci gaba daga wani karnin jarumai zuwa wani karnin. Yace ga mahalartan, wannan wata tunatarwa ce mai muhimmanci cewa ayyukan mu ba zasu kammalu ba har sai mun gano su duka, koda kuwa zai dauki tsawon lokaci.
Korea ta Arewa bata bada wani karin bayani da zai taimaka wurin gano daidaikun gawarwakin ba da ake dawowa dasu zuwa Amurka, a cewar wani jami’in tsaron Amurka a hirarsa da Muryar Amurka.
Facebook Forum