Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Za Ta Hana Shiga Da Shinkafa Da Wasu Kayayyaki Cikin Kasar


Kayan abinci
Kayan abinci

Ministan ciniki da masana'antu, Kobena Tahir Hammond, ya sanar da wani muhimmin mataki da gwamnatin Ghana ta dauka na samar da dokar hana shigowa da kayayyaki sama da 20, ciki har da shinkafa da wasu kayayyakin da ake amfani da su a Ghana.

Da yake karin haske kan dalilin wannan tsarin, Ministan ya jaddada makudan kudaden da Ghana ta ke kashewa, kimanin dala miliyan 164, kan wadannan kayayyakin da ake shigowa da su.

Ya kuma jaddada mauhimmancin wannan matakin shi ne bunkasa ci gaban fannin harkokin noma da tabbatar da samun isasshiyar shinkafa domin gujewa karancin abinci da talauci a Ghana.

Taro
Taro

Mallam Jafaru Dankwabia mataimakin daraktan bincike kan yanayi da samar da abinci, a tsokacin sa ya ce, "idan an aiwatar da wannan dokar hana shigowa da shinkafa, sai kasar ta gaza samar da shinkafa, toh Ghana za ta fuskanci tsadan shinkafa, za'a samu masu shigowa da shinkafar ta barauniyar hanya, wanda hakan zai haifar da rashin kudi a kasar. "

Kayan abinci
Kayan abinci

Malam Hamza Attijani masani tattalin arziki ya ce, Ghana dai tana dogaro da ruwan sama ne wajen harkokin shuka, idan tana so ta yi dogaro da kanta, sai ta bullo da dabarun wanda ba za ta dogara da ruwan sama ba.

Ita kuwa Malama Aisha mai saida shinkafa cewa ta yi, matakin Gwamnati na hana shigowa da shinkafa zai kawo cikas a kasuwancinsu, saboda shinkafar Ghana ba ta da kasuwa akan na kasashen waje.

Saurari rahoton Hawawu Abdul Karim Young Pioneer:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG