Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karamin Yaro Ne Yai Sanadiyyar Gobarar Da Ta Kashe Mutane 12


'Yan Kwana Kwana a wajen gobarar

Bincike ya gano cewa yaro karami ne ya haddasa gobarar da ta kashe mutane da dama a Birnin New York.

Shugaban 'yan kwana kwanan New York Daniel Nigro jiya alhamis yace gobarar da ta kashe mutane 12 a wani gini a unguwar Bronx ta soma ne sanadiyyar wasan da wani yaro dan shekara uku yayi da risho.

Ya shaidawa manema labarai yau jumma'a cewa mahaifiyar yaron da shi da wani dan nata sun fice daga gidan, ta bar kofar gidan nasu a bude daga bisani wutar ta yadu zuwa sauran gidajen.

'Yan kwana kwana sun isa wajen a cikin mintuna uku kuma Nigro ya baiyana rashin rayukan da akayi a sanadiyyar gobarar a matsayijn mafi muni da aka taba gani cikin shekaru 25 a birnin NewYork.

Jami'ai sunce kimanin 'yan kwana kwana 170 ne suka yi aikin kashe wutar tare da ceton wadanda abin ya ritsa dasu, sun kara da cewa a kalla mutane 4 ne sukaji munana raunika.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG