Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Hallaka Mutare 6 Iyali Daya a gombe


Wutar Gobara

Wata Yarinya ‘yar shekaru bakwai ta tsallake rijiya da baya a wata gobara da ta lakumi dukan mutanen iyalin su shida .

Gobarar da tayi sanadiyar mutuwar wani mutum da matarshi mai ciki da kuma ‘ya’yanshi biyar ta tashi ne a wata unguwa da ake kira Alkahira a yankin Arawa dake jihar Gombe.

A cikin hira da Muryar Amurka, wani dan’uwan mamacin ya bayyana cewa, maigidan dake aiki a wani gidan mai, ya dawo gida da yamma ya tarar an dauke wutar lantarki. Bayan sun kwanta da dare aka kawo wuta da misalin karfe goma sha daya na dare sai gobara ta tashi. Ya bayyana cewa, gobarar ta lashe komi a cikin gidan

Karamar yarinyar ta tsira ne lokacin da ta fita tana kwankwasawa makwabta kofa domin neman taimako, yayinda mahaifinta ya shiga inda sauran ‘yan’uwanta suke kwance yayi kokarin fitar dasu ta bayan gida amma hayaki ya turnuke dakin, suka kasa fita dukansu suka gamu da ajalinsu.

Yanzu haka dai yarinyar da ta tsira daga gobarar tana zama da kakarta.

Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa Abdulwahab Mohammed ya aiko daga Bauchi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG