Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara ta Lakume Katafaren Kantin Kayayyakin NEXT Cash & Carry a Abuja


Katafaren katin siyayya na NEXT CASH & CARRY da Gobara ta lakume

Jami'an hukumar kashe gobara a birnin Abuja sun yi kira ga jama'a da su lura su kuma guji zuwa wurin da gobarar ke ci.

Da safiyar yau Lahadi 26 ga watan Disamba ne gobara ta tashi a katafaren kantin saida kayayyaki na NEXT Cash & Carry da ke kan hanyar titin Ahmadu Bello zuwa Kado-kuchi a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

A yanzu haka dai ma’aikata daga hukumar kashe gobara ta tarayya suna kan kokarin kashe gobarar kuma sun shawarci mazauna yankin da su guji bin wuraren da ma’aikatan ke aikin kashe gobarar a wani mataki na hana yaduwarta, a cewar jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Mrs. Ugo Huan, la’akari da wannan lokaci na bukukuwan Kirsimeti ana sa ran mutane su ziyarci wajen don siyayya.

Katafaren kantin saida kayayyaki na NEXT Cash & Carry da Gobara ta lakume
Katafaren kantin saida kayayyaki na NEXT Cash & Carry da Gobara ta lakume

Huan ta ce ma’aikatan kashe gobara daga shiyyoyi dabam-daban, har da hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya Abuja, suna can suna fafatawa a aikin kashe gobarar.‘

Sai dai kawo yanzu ba’a san musabbabin gobarar ba.

Dubi ra’ayoyi

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG