Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Wani Basaraken Gargajiya a Jihar Filato


Fulani masu garkuwa da mutane
Fulani masu garkuwa da mutane

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Charles Mato, Sum Pyem din garin Gindri. Jami'an tsaron jihar sun ce an kaddamar da binciken gano inda yake da ceto shi.

A yau Lahadi ne wasu ‘''yan bindiga suka sace basarake Charles Mato daga gidansa da ke garin Gindiri a karamar hukumar Mangu a jihar Filato.

Manjo Ishaku Takwa, jami'in yada labarai na rundunar sojin wanzar da zaman lafiya da ake kira Operation Safe Haven a jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Jos, inda ya ce an yi garkuwa da Mato ne daga gidansa.

Takwa ya ce an tattara dakarun da ke aiki a yankin domin gudanar da bincike da kuma aikin ceto basaraken.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan matsala ta garkuwa da sarakuna ba, sai dai a yanzu lamarin na dada kamari duk kuwa da kokarin da jami’an tsaro ke yi .

XS
SM
MD
LG