Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Tashi A Wata Babbar Kasuwar Sayar Da Kayan Wasan Wuta Na Kirsimeti


Wata gaguramar wuta ta tashi a wata mashahuriyar kasuwar saida kayan wasan hasken wuta ko kuma fireworks a turance, a kusa da Birnin Mexico inda tayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 31, 70 kuma suka raunata.

Kasuwar Mai suna San Pablito dake birnin Tultepec tana tazarar kilomita 30 arewa da babban birnin, tana makare da masu sayayyar kayan wasan wutar domin bukukuwan Kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Ofishin babban alkalin kasar yace abubuwa shida ne suka fashe wadanda suka jawo hadarin, kuma sun kaddamar da bincike akan keta dokoki da ka’idojin sayar da kayan wasan wutar domin gano wanda ke da alhakin hadarin.

Shugaban kasar Mexico Enrique Pean Nieto yayi amfani da shafin twitter domin aikawa da ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da kuma fatan neman sauki ga wadanda suka ji raunuka.

Fashewar da kuma gobarar ta lalata rumfuna da yawa a shekarar 2005 da kuma 2006.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG