Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Sun Ci Gaba Da Farautar Mutumin Da Ya Kai Hari A Kasar Jamus


Jami'an tsaro a kasuwar da aka kai hari
Jami'an tsaro a kasuwar da aka kai hari

A yau laraba Hukumomi a kasar Jamus suka ci gaba da farautar mutumin da ya tuka motar a kori kura cikin wata kasuwa Kasuwar sayar da kayan Kirsimeti dake cike da jama'a a birnin Berlin, kwana daya bayan sakin wani mutum da aka kama, ba da dadewa ba bayan kai wani hari da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane 12.

Kafofin yada labarai na Jamus sun ce jami’an Yan sanda na neman mutumin dan kasar Tunisia sakamakon Takardun da aka samu a Motar.

Yan sandan Na Berlin sun samu bayanai kusan 500 daga wayar tarho tun daga lokacin da al’amarin ya faru a ranar Litinin.

Kungiyar Da’esh tayi ikirarin cewa, harin ya biyo bayan kiran da tayi ne ga jama'a da su kaiwa fararen hula hari a kasashen da suke cikin kungiyar hadin gwuiwar da Amurka ke jagoranta da nufin murkushe kungiyar Yan Ta’adda.

Kasar Jamus bata cikin kasashen da suka aiwatar da hare haren jiragen sama akan Yan Kungiyar ta DA’esh a Iraqi da kuma Syria, Amma tana taimakawa da ya hada da Kara Mai a ababawan hawa da kuma Lalubo inda Yan kungiyar ta Da’esh suke.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG