Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobarar Asibiti Ta Hallaka Mutane A Koriya Ta Kudu


'Yan Kwana-Kwana A Asibitin Da Gobara ta tashi

Wata mummunar gobara ta tashi a wani asibitin da ke kasar Koria ta Kudu har ta hallaka mutane da dama ta kuma bar jama'a da taraddadin yawan matattun na iya karuwa sakamakon jikkatar da wasu suka yi.

Akalla mutane 41 suka rasa rayukansu a cikin wata mummunar gobarar da ta tashi a wani asibiti da ke kasar Koriya ta Kudu. Ana kuma fargabar cewa da kyar in yawan matattun ba zai karu ba a nan gaba.

Ko bayan wadanda suka rasa rayukansu, har ila yau akwai mutane kamar 70 da suka ji rauni, 10 daga cikin wadanda suka jikkatan suna da raunukan kuna a jiki masu barazana ga rayuwarsu.

Ma’aikatan kashe gobara sun ce, wutar ta tashi ne daga wani dakin tiyata na asibitin Sejong dake garin Miryang mai tazarar km 300 daga Seoul babban birnin kasar. Rahotanni sun ce, kamar marasa lafiya 200 ne ke kwance a asibitin lokacin da al’amarin ya faru.

Shugaban Koriya ta Kudu Moon-Jae-in ya kira taron gaggawa da mukarrabansa don tabbatar da cewa an dauki duk matakan da suka dace don taimakawa wadanda gobarar ta shafa.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG