Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karfin Shiga Internet Daga Blom-Blom? Google Yace Hakika!!


Alamar kamfanin Google

Masana kimiyya dake aiki da kamfanin Google sun culla maka-makan ledoji shigen blom blom da aka durawa iskar da ake kira helium a turance, kamar guda 30 cikin sararin samaniya.

Masana kimiyya dake aiki da kamfanin Google sun culla maka-makan ledoji shigen blom blom da aka durawa iskar da ake kira helium a turance, kamar guda 30 cikin sararin samaniya a kasar New Zealand.

shirin wanda na gwaji ne kamfanin yana fatar idan kome ya kankanma ta hakan zai samar da intenet ga mutane milyan dubu biyar aduk fadin duniya, wadanda ahalin yanzu basu da damar shiga yanar gizon.

A ranar Asabar, babban kamfanin harkokin fasahar internet din ya kaddamar da wannan shiri a birnin Christchuch dake New Zealand inda masu gidaje da suka amince da agwada shirin da gidajensu suka fara samun karfin internet a computocinsu daga blom blom da aka culla sama.

Ledojin wanda iska ce take rike dasu zasu cigaba da shawagi da nisan kilomita 20 daga doron kasa, kuma an tsara ta yadda zasu dore a can sama na tsawon lokaci sama da wata uku.

Shugaban kula da shirin Mike Cassidy yace injiniyoyi suna fatar samar da sukunin shiga internet kan kudi mai rahusa a duk fadin duniya musamman a sassan da basu sami cigaba ba. Ya bada misalain da wasu sassan Afirka masu yawa inda kudin shiga internet yake dara albashin wata daya.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG