Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Iran Sun Tabbatar Da Zaben Hassan Rowhani, Sabon Shugaban Kasar


Sabon shugaban kasar Iran Hasan Rowhani.

Ministan harkokin cikin gida na Iran Mostafa Mohammed Najjar, ya ayyana malamin addinin Islama mai sassaucin ra’ayi, Hassan Rowhani, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Ministan harkokin cikin gida na Iran Mostafa Mohammed Najjar, ya ayyana malamin addinin Islama mai sassaucin ra’ayi, Hassan Rowhani, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, nasarar da ta bada mamaki ganin ya doke ‘yan takara masu mulkin kasar masu ra’ayin rikau.

Rowhani wanda yake da farin jini wajen ‘yan kawo canji, kuma tsohon wakilin Iran a shawarwari kan harkokin nukiliyar kasar, ya sami kusan kuri’u milyan 19, cikin kuri’u milyan 37 da aka kada. Da kadan ya zarce kashi 50 cikin dari d a ake bukata, wanda hakan ya kauda buktar a zaben fidda gwani. Dan takara dake bi masa a can baya shine magajin garin Tehran Mohammed Bagher Qalibaf, wanda ya sami kamar kashi 16 cikin dari na kuri’u d a aka kada.

Babban sakataren MDD Ban ki-moon ya taya Rowhani murna, daga nan ya nemi hukumomin kasar da shugaban mai jiran gado su “taka muhimmiyar rawa mai ma’ana” a harkokin yankin da kuma duniya baki daya.

Amurka ma tana yiwa al’umar Iran barka saboda shiga cikin ahrkokin zaben kasar, kakakin fadar White House Jay Carney yace gwamnatin shugaba Obama tana mutunta kuri’ar da suka yi. Duk d a haka sanarwar da Mr. Carney ya bayar ta kuma lura d a cewa an gudanar da wannan zabe ne cikin wani yanayi na “dungun da gwamnati take yi, da dabai ba yi, da kuma rashin tafiyar da zaben a zahiri, sakawa ‘yan jarida takunkumi da kuma yanayi na rashin walwala saboda matsin lamabar jami’an tsaro.
XS
SM
MD
LG