Idan kuna biye damu shirin Domin Iyali yana neman hanyar shawo kan matsalar aurar da 'yaya mata da wuri a Jamhuriyar Nijar inda bincike ya nuna, ana aurar da kashi saba'in cikin dari na 'ya'ya mata a kasar kafin su cika shekaru goma sha takwas. Shirin ya hada kan masu ruwa da tsaki domin gano inda wannan dabi'a ta sami asali da kuma matakan da za a iya dauka na shawo kanta. Ga kashi na biyu na tattaunawar da wakilinmu Sule Mummuni Barma da ya jagoranta.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.