Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Satumba 27, 2018: Damawa Da Mata A Harkokin Siyasa, Kashi Na Biyu


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Madam Rebecca Sharibu, Mahaifiyar Leah Sharibu dalibar makarantar sakandaren 'yanmmata ta Dapchi daya tilo da ta rage a hannun kungiyar Boko Haram, ta musanta rahotannin da wadansu jaridun Najeriya suka buga jiya Laraba cewa, ta yi karar gwamnatin tarayya tana neman diyyar Naira miliyan dari biyar da kuma bukatar a saketa ba tare da wani sharadi ba.

Bisa ga rahoton, banda gwamnatin tarayya, karar da aka shigar ta hadin guiwa ta hada da sifeta janar na 'yan Sanda, Mr. Ibrahim Idris da babban lauyan gwamnatin tarayyar, Mr. Abubakar Malami sabili da gaza ceto 'yarta. Rahoton ya bayyana cewa, an shigar da karar ne ranar goma sha tara ga wannan watan na satumba a wata kotu dake birnin Iko da lambar shigar da kara- FCH/L/cs/1528/18, aka kuma ambaci wani mai suna Mr. Daniel David Kadzai da kuma,Dr. Adeniyi Ojutiku, Darektan wata kungiya mai zaman kanta da ake kira the Lift-Up-Now Incorporation, dake Amurka a cikin masu shigar da karar.

Sai dai da Shirin Domin Iyali ya tuntubi mahaifin Leah Nathan Sharibu da dai aka wallafa wannan rahoton a yanar gizo jiya da asuba, sai ya bayyana cewa shima ganin labarin yayi kamar yadda muka gani bashi da wata masaniya a kai, ya kum ayi alkawarin cewa zai gudanar da bincike kafin ya tuntube mu, sai dai kawo lokacin hada wannan shirin bamu ji daga gareshi ba.

A cikin hirarta da tashar labarai ta CNN,- kamar yadda CNN ta wallafa a shafinta na twitter, mahaifiyar Leah tace bata da wata masaniya game da wannan batun, sai dai tana ganin wadansu ne suke aron bakinta suna cin albasa.

https://twitter.com/CNNAfrica/status/1044917897062240256?ref_src=twsrc%5Etfw

Banda batun Leah, wadansu jaridun kuma sun buga cewa, ranar goma ga wannan watan Lauya Funmi Falana ta kamfanin aikin lauya na fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakin bil'adama a Najeriya, Falana & Falana, ta shigar da kara a babbar kotu dake Abuja, a madadin sauran 'yammatan Chibok dari da goma sha biyu da har yanzu suke hannun kungiyar Boko Haram, tana nema a tursasawa gwamnati ta gaggauta ceto su, ta kuma rika bada bayanai kowanne wata kan halin da ake ciki. FHC/ABJ/CS/913/2018

Shirin Domin Iyali zai bi diddigin wadannan rahotanni nan gaba domin neman karin bayani da kuma duk wata ci gaba da aka samu.

Yau dai zai dora ne a kan batun da muka fara bibbiya a kai makon jiya, da ya shafi damawa da mata a harkokin siyasa, da kuma neman cika alkawarin da Najeriya tayi na basu kashi talatin da biyar cikin dari na mukaman siyasa, lamarin da ya kai ga mata suka yi gangami jiya a jihar Kano.

Yau ma muna tare da Barrister Badiha Abdullahi Mu'azu 'yar gwaggwarmayar kare hakin bil'adama, da Hajiya Hauwa El-Yakub mai neman tsayawa takarar majalisar dattijai karkashin tutar jam'iyar NPM domin wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, sai kuma, Kwamred Sa'idu Kabiru Dakata darektan cibiyar wayar da kan al'umma game da shugabanci na gari.

Saurari shirin domin jin bayanansu.

Damawa da mata a siyasa Pt2-10:35"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:35 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG