Bayanda gwamnatin tarayya ta sanar a watan Mayu cewa, ta ciyar da yaran makaranta miliyan bakwai da dubu dari hudu jihohi ishirin da biyu na Najeriya, yayinda shirin ya samar da aikin dafa abinci ga mata sama da dubu saba’in da biyar, shirin Domin Iyali na zaga wadansu jihohin arewacin Najeriya inda aka fara aiwatar da shirin domin nazarin nasarori da kuma kalubalai da shirin ke fuskanta.
Yayin wannan ziyarar gani da idon ne kuma muka tarar ana rabawa yara abinci a takarda a wata makaranta dake birnin Kano. Mun debi wadansu bangarorin hirarrakin da muka gabatar a shirin da muka dauki makonni muna bibiya a kai da ya kunshi jihohin Plato da kuma Kano.
Shirin Domin Iyali ya kuma yi bibiya kan batun damawa da mata a harkokin mulki. Inda muka gayyaci masu ruwa da tsari domin neman hanyoyin cimma wannan burin.
Saurari shirin domin jin kadan daga cikin abinda muka gabatar. Ana kuma neman shirin baki daya ta yanar gizo a wannan shafin na Sashen Hausa.
Kadan ke nan dake cikin batutuwa da dama da muka tabo a shirin Domin Iyali da suka shafi kula da jin dadin iyali da ci gaban kasa a wannan shekara ta dubu biyu da goma sha takwas dake karewa. Zaku iya sauraron dukan wadannan shirye shiryen a daya a shafinmu na internet VOAhausa.com
Facebook Forum