Accessibility links

Gwamnan Jihar Borno Ya Kira Mutanen Jihar Su Shiga APC


Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima,

Ranar Larabar da ta gabata jam'iyyar adawa ta APC ta fara yin ragistan 'ya'yanta a duk fadin Najeriya har da jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Kamar sauran jihohin Najeriya a jihar Borno ma APC ta fara yiwa 'ya'yanta ragista ranar Larabar da ta gabata.

Gwamnan jihar Kashim Shettima shi ya fara yin ragista a matsayinsa na zama jagoran jam'iyyar APC a jihar. Ragistar ta ba gwamnan zama cikakken dan jam'iyyar APC. Bayan ya yi ragista ya umarci duk mutanen jihar su fito kwansu da kwarkwatarsu su shiga jam'iyyar APC wadda ya ce jam'yyarsu ce kuma dole su riketa da hannuwa biyu.

Gwamnan ya yi addu'a Allah ya ba jihar zaman lafiya domin idan babu zaman lafiya ba za'a samu cigaba ba kuma a jam'iyyance ba zasu iya kawo taimakon da suke so su baiwa jama'a ba. Ya sake jaddada cewa burinsu shi ne su taimakawa mutane. Dangane da koke-koke da wasu ke yi ya ce dukansu 'yan gida daya ne domin haka zasu shawo kan duk wata matsala. Ya ce a siyasa dole a samu kananan matsaloli.

Alhaji Usman Majidadi Kumo yana cikin mukarraben gwamnan shi ma ya yanki nashi katin. Ya ce da yankar katin shi ya karbi 'yancinsa domin shi ne masomin canji a kasar. Yin ragistan shi ne irinsa na farko tun da aka kafa jam'iyyar wajen watanni bakwai da suka gabata.

XS
SM
MD
LG