Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan jihar Plato Simon Lalong ya yi bukin sallah a Daura

Gwamnan jihar Plato ya yi bukin Sallar layya a Daura tare da shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi kira da a zauna lafiya domin ci gaban kasa.

Gwamnan Lalong ya bayyana cewa, yaje bukin sallah a Daura ne domin yiwa shugaba Muhammu Buhari barka da Sallah da kuma fatar alheri.

Gwamnan ya kuma kaiwa Mai Martaba Sarkin Daura Dr. Umar Faruk gaisuwar caffa inda ya halaraci nadin sarautar gwamnan jihar abija Orji Uzo Kalu a matsayin Dan Baiwan Kasan Hausa.

Da yake ganawa da manema labarai, gwamna Lalong yace Najeriya ba zata iya cin gaba, a kuma sami inganta rayuwar talakawa yadda ya kamata ba sai an sami zaman lafiya.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG