Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Myanmar Ta Kira 'Yan Rohingya Gida


Yaran Rohingya na buga kwallo a Cox's Bazar, Bangladesh.
Yaran Rohingya na buga kwallo a Cox's Bazar, Bangladesh.

Shekara guda bayan da dubban Musulman Rohingya suka tsere wa tsauraran matakan soji, zuwa Bangladesh dake makwaftaka da su, Gwamnatin kasar Myanmar ta ce kasar ta tayi lafiya kuma wadanda sukai gudun hijira zasu iya dawowa, saidai wadansu kungiyoyin kasa da kasa basu amince da hakan ba.

Wadanda suka tsira daga munanan matakan sojin a watan Agustan shekarar 2017 sun shaidawa masu aikin agaji a Bangladesh irin ta’asar da aka musu, wanda suka kunshi yi wa ‘yan uwansu fyade da kashe su a gaban su da kuma kone kauyakun su duk dan kar su sake komawa wajen.


Mutanen Rohingya dubu dari biyar ne suka yi gudun hijira zuwa Bangladesh a watan farko kana kimanin dubu dari biyu suka biyo baya a sauran wataninn. Yanzu haka suna zaune Cox Bazar, sansanin ‘yan gudun hijirar da ya fi kowanne girma da yawan mutane a fadin duniya.


“ Wannan wani abu ne da zamu bayyana a matsayin kisan kiyashi da nufin shafe wata kabila” a cewar Adama Deing, babban mai bada shawara a majalisar dinkin duniya kan hana kisan gilla, Kalaman nasa sun yi daidai da abinda shugabansa , babban sakataren MDD Antonio Guterres da kuma babban kwamishinan kwato ‘yancin bi’adama Zeid Ra’ad Al Hussein suka fada tun farko.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG