Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsofaffin Jami'an Gwamnatin Amurka Da Na Yanzu Suna Shirin Jana'izar Sanata McCain


Ranar Lahadi za a yi jana’izar marigayi Sanata John McCain a kwalejin sojojin ruwan Amurka dake Annapolis, jihar Maryland.

Wasu jami’an gwamnatin Amurka a yanzu da na baya daga fannonin siyasa dabam dabam na shirin halartar taron makokin Sanata John McCain wanda za a yi ranar Asabar, daya daga cikin tarurruka na karshe da ake shirin yi don karrama dadadden dan majalisar wanda ya rasu ranar Asabar da ta gabata yana da shekaru 81 da haihuwa.

A taron da za a yi a majami'ar kasa da ake kira National Cathedral dake birnin Washington, tsohon shugaba Barack Obama, da tsohon shugaba George W Bush za su yi jawabai. Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger da Sanata Joseph Lieberman suma za su yi jawabi.

Wadanda zasu raka akwatin gawar sune tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da tsohon sakataren ma’aikatar tsaro William Cohen, da tsohon magajin garin birnin New York Michael Bloomberg, da kuma tsofaffin Sanatoci, Gary Hart, da Russell Feingold da kuma Phil Gramm.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG